Sauran mutanen da rundunar ta cafke sun hada da wadanda ake zargi ’yan fashi ne da barayi da masu aikata fyade da ’yan sara-suka da dai sauransu.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Abdu Umar, ya tabbatar da hakan yayin gabatar da wadanda ake zargin a ranar Talata a hedikwatar ’yan sandan da ke birnin Maiduguri.
Ya ce an gurfanar da mutum 67 daga cikinsu a gaban kotu tare da tisa keyarsu zuwa gidan gyaran hali.
Kwamishinan ’Yan Sandan ya bayyana yadda aka cafke wasu da suka yi wa wata yarinya mai shekara 13 fyade.