Majalisar Wakilai ta fara kokarin yin amfani da karfin ikonta kan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari game da sashe na 84(8) na Dokar Zabe ta Kasa da ke magana kan daliget na alfarma.

Yunkurin ya zo ne bayan Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar, Toby Okechukwu da dan majalisa Ben Ibakpa suka gabatar a zauren majalisar ranar Laraba.


’Yan majalisar sun yi korafin cewa wasu daga cikin tanade-tanaden sassan dokar na da tarnaki kamar yadda aka gani yayin zabukan fitar da gwani da jam’iyyu suka kammala a kwanan nan.


A cewar Mataimakin Shugaban Marasa Rinjayen, dole ne majalisar ta kammala aikin da ta fara na samar dokar da za ta kawo sauyi ga ilahirin yadda ake gudanar da zabe a Najeriya.


A nasa bangaren, Ben Ibakpa ya ce an kira su daga mazabunsu daban-daban ana yi musu korafe-korafe a kan sassan dokar.


Sai dai bayan sun gama gabatar da kudurorin nasu, Shugaban Majalisar, Femi Gbajabiamila, ya tunatar da su cewa ko da yake wa’adin kwana 30 da majalisar ke da shi kafin Shugaban ya sa hannu a gyaran ya kare, har yanzu akwai ragowar matakan da ya kamata a bi kafin a kai ga daukar matakin.


Idan za a iya tunawa, a ranar Talatar da ta gabata ce Shugaban majalisar ya zargi tsarin daliget na zaben fitar da gwani da cewa shi ne ummul-aba’isun da da yawa daga cikin ’yan majalisar suka gaza samun tikitin dawowa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *