Mai tsawatarwa a majalisar dattijan tarayya, Ori Uzor Kalu, ya bayyana cewa da kamar wuya jam’iyyar APC ta lashe zaben shugaban kasa idan bata dauki mataimaki Musulmi daga Arewa ba.

Kalu ya ce yanzu ya zama wajibi Tinubu ya dauki Musulmi muddin yana son lashe zabe a 2023.


Dan siyasan yace jam’iyyar APC na tsaka mai wuya yanzu.
Ya bayyana halkan ne ranar Laraba yayinda yake hira da manema labarai a majalisar dokokin tarayya Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *