Kungiyar kamfanonin jiragen sama ta kasar nan ta bayyana fargaba cewa mambobinsu guda uku na iya daina aiki gaba daya sakamakon karancin man fetur.

Duk da cewa kungiyar ta sakaya sunayen kamfanonin uku, amma mataimakin shugaban kungiyar Mista Allen Onyema ya ce tsadar man da jirgin sama ke amfani da shi mai suna Jet A1 ya kai naira 714 ga kowace lita guda.


Rahotanni sun bayyana cewa tattaunawar da kungiyar ta yi da gwamnain tarayyar Najeriya ba ta haifar da wani abin a zo a gani ba.


Mista Onyema ya kuma ce wata 16 da ya gabata, farashin man na Jet A1 bai wuce naira 200 ga lita ba ba, amma yanzu ya zarce naira 700 ga kowace lita a kasuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *