A ranar Alhamis, 16 ga watan Yuni 2022, ta ce an kai Gwamnan jihar Edo kara ne a kotun ma’aikata na kasa da ke Benin.
Yan reshen kungiyar ASUU na jami’ar Ambrose Alli ne suka kai karar Godwin Obaseki gaban babban kotun, su na kalubalantar matakan gwamnati.
Malaman jami’ar sun ce dakatar da aikinsu da Gwamna ya yi, ya sabawa doka, kuma ya ci karo da kundin tsarin mulki, don haka aka nemi dole a janye ta.
Bayan kungiyar ASUU ta shiga yajin-aiki, sai gwamnatin Edo ta bakin SSG watau Osarodion Ogie, ta bada sanarwar dakatar da ayyukan kungiyar a jihar.
Kamar yadda Sakataren gwamnatin jihar ya bayyana, an bada umarni a daina biyan malaman jami’ar albashi saboda sun kauracewa wuraren aikinsu.
Abin har ya kai Ogie yana cewa wadanda suka tafi yajin-aikin sun rasa ayyukansu, ya kuma bada sanarwar ana neman wadanda za su iya cike gurabensu.