Miyagun ‘yan bindigan da suka dauke wasu mutane 29 da suka halarci taron daurin aure a ranar Asabar a garin Sokoto sun bukaci a biya Naira miliyan 145 kudin fansa.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigan sun bukaci a biya Naira miliyan 145 kafin mutane nan 29 da suka shigo hannsu, su iya komawa gidajensu.


Mafi yawan wadanda ‘yan bindigan suka dauke, su na saida wayoyi ne a kasuwar wayar salula na Bebeji Communication Market a Gusau, jihar Zamfara.


Sakatare-Janar na kungiyar masu saida waya a kasuwar, Nasiru Musa, ya shaida cewa ‘yan bindigan sun tuntube su a waya a farkon makon nan. Wadannan miyagu sun lafta fansar Naira miliyan 5 ne a kan kowane mutum guda.


A lokacin da ‘yan bindigan suka kai hari, mutane kusan 50 aka yi tunanin cewa an yi gaba da su.


Daga baya an samu labarin wasu da aka dauke sun dawo gida, sannan ‘yan banga da ke aikin sa-kai sun yi nasarar ceto wasu mutane bakwai daga mahalartam.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *