Kuɗaɗen da za a ciyo bashin, za a yi amfani da su wajen sanya na’urorin CCTV domin kyautata tsaro a jihar.
Amincewar ciyo bashin ta biyo bayan wasiƙar da gwamnan ya aikewa majalisar wadda shugabanta Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari ya karanta a zaman majalisar na ranar Laraba.
Ta cikin wasiƙar gwamna Ganduje ya ce, za a sanya na’urorin ne la’akari da barazanar tsaro da jihar ke fuskanta a ƴan kwanakinnan.
Wakilin Freedom Radio a majalisar Auwal Hassan Fagge ya ruwaito cewa, bayan tattauna batun ne tare da bada shawarwari ƴan majalisar suka amince a ciyo bashin.