Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodinma ya ce babu wani wuri a kundin tsarin mulkin Najeriya da ya hana dan takarar shugaban kasa Musulmi daukar mataimakinsa Musulmi.

Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodinma ya ce babu wani wuri a kundin tsarin mulkin Najeriya da ya hana dan takarar shugaban kasa Musulmi daukar mataimakinsa Musulmi a daidai lokacin da ‘yan Najeriya da dama ke adawa da duk wani yunkuri na gabatar da ‘yan takarar zabe mai zuwa daga addini guda.


Uzodinma ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa ‘dan takarar zaben shugaban kasa ko gwamna zabin wanda yake so ya mara masa baya wajen duba cancantarsa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, amma kuma babu wani wuri da ya yi maganar addini.


Gwamnan ya ce, a daidai lokacin da ake bukatar hadin kan Najeriya, abin dubawa shi ne cancanta da kuma kalubalan da ke gaban ‘yan takarar dangane da nauyin da ke kansu na samar da romon dimokiradiya da kuma sanya kasar ta ci gaba kamar sauran kasashen duniya, maimakon yankin da ‘dan takara ya fito ko addininsa.


Uzodinma ya ce ya dace ‘dan takarar Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya duba batutuwan da za su sa shi ya samu nasara domin shi ne babban abin da ya dace ya sanya a gaba amma ba addini ba.


Gwamnan ya ce yankin da ya fito na kudu maso gabas baya bukatar mataimakin shugaban kasa sai dai shugaban kasa, saboda haka ya dace su hada karfi da karfe wajen marawa Tinubu baya.


Wannan matsayi na Uzodinma ya ci karo da na kungiyar Kiristocin Najeriya da kuma wasu jama’a daga sassa daban daban na kasar da suke ganin cewar adalci ne Tinubu ya dauki Kirista a matsayin wanda zai mara masa baya.


Hukumar zaben Najeriya ta sanya ranar 17 ga watan Yuni ga duk wata jam’iyyar siyasar Najeriya ta gabatar da sunayen ‘yan takarar zabe mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.