Wata kotu a jihar Kano zata yanke hukunci kan makashin Hanifa Abubakar ranar 28 ga watan Yuli.

Babbar Kotun Kano da ke zamanta a Audu Baƙo, ta sanya ranar 28 ga watan Yuli, 2022 domin yanke hukunci kan shari’ar kisan Hanifa Abubakar, yar shekara biyar.

Ana zargin shugaban makarantar da Hanifa ke karatu, Abdulmalik Tanko, da garkuwa haɗe da kisan yarinyar

Alƙalin Kotun, Mai shari’a Usman Na’abba, ya zaɓi ranar ne a zaman ranar Talata bayan zartar da jawabin rubutu na ƙarshe da kowane ɓangarori suka yi.

Gwamnatin Kano ta gurfanar da mutum uku; Abdulmalik Tanko, tare da waɗan da suka haɗa kai, Hashin Isiyaku, da Fatima Jibril Musa, gaban Kotun bisa tuhume-tuhume guda biyar.

Tuhume-tuhumeɓ sun haɗa da haɗa kai wajen aikata babban laifi, garkuwa, ɗaurin wuri ɗaya da kuma mummunan kisan kai wanda ya saba wa sashin 97, 274, 277, 221 na kundin fanel kod.

A zaman na yau Talata, lauya mai gabatar da ƙara, Lamido Abba Soron Dinki, ya roƙi Kotun ta duba hujjojin da aka baje mata ta tabbatar da laifin waɗan da ake ƙara kuma ta yanke musu hukuncin kisa. A jawabinsa ya ce:

“Muna rokon Kotu ta yanke musu hukuncin kisa su duka saboda hukuncin waɗan nan sashin da ake tuhumar su da saɓa wa ya kunshi hukunci ɗaya ne kisa.”

Lamido Abba Soron Dinki

Rahma media ta tattaro muku cewa a ranar 4 ga watan Disamba, 2021 aka sace Hanifa yayin da take kan hanyar komawa gida daga Islamiyya kuma daga baya aka gano cewa an kashe ta.

Da farko, Tanko ya amince ya yi amfani da maganin Ɓera na N100 wajen kasheta da ɓinne ta a ɗaya daga cikin makarantunsa, amma daga baya ya canza magana da cewa sace ta kaɗai ya yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *