Wasu ’Yan bindiga sun kwashi kashinsu a hannun jami’an tsaro a kan Babbar Hanyar Kaduna zuwa Abuja, a lokacin da suka yi yunkurin yin garkuwa da matafiya

Jami’an tsaron hadin gwiwar sun ragargaji ’yan bindigar tare da kashe daya daga cikinsu a musayar wuta da suka yi a lokacin da jami’an tsaron suka kai dauki bayan ’yan bindigar sun kai wani hari kan matafiyan .


Kakakin ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige ya ce, “Jami’an tsaron sun yi nasarar kwato bindiga kirar AK47 da harsasai da kuma babur din ’yan bindigar.


Ya ce ganin irin ragargazar da jami’an tsaron suka yi musu, sai ’yan bindigar suka ranta a na kare zuwa cikin daji.
Ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, Yekini Ayoku, ya yaba wa jami’an tsaron bisa wannan namijin kokari, tare da ba su tabbacin cewa ba za a taba mantawa da abin da suka yi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *