Wannan dai na zuwa ne yayin da wa’adin da Hukumar Zabe ta kasa INEC ta debar wa jam’iyyu domin mika mata sunayen ’yan takarar Mataimakin Shugaban Kasa, inda jam’iyyun ke ci gaba da fadi-tashi domin ganin cewa ba su yi zaben tumun dare ba.
Hukumar INEC dai ta ce duk jam’iyyar da ba ta mika sunan abokin takarar masu neman kujerar Shugaban Kasa ba zuwa ranar 17 ga watan Yuni, to za a hana ta shiga Babban Zaben na bana Aminiya ta ruwaito cewa jam’iyyar APC da PDP sun takaice zabin abokan takararsu zuwa wasu manyan ‘yan siyasa.
Wata majiya mai tushe ta ce bangaren dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Ahmed Bola Tinubu ya takaice a kan Sanata Kashim Shettima, tsohon gwamnan Jihar Borno, yayin da kuma magoya bayan dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, sun kammala tattaunawa kan a tsayar da gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matasayin abokin takarsa.
Sai dai kuma wasu majiyoyi sun shaida cewa jiga-jigan tsohuwar jam’iyyar CPC wadda tana cikin jam’iyyun da suka zama tsintsiya madauri daya aka samar da jam’iyyar APC, na shirin tuntubar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari domin ya ba da shawarar a tsayar da Ministan Shari’ar wato Malami, ko kuma Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika.
Bayanai sun ce an shirya ganawa tsakanin Tinubu da Shugaba Buhari a ranar Laraba, kuma batun abokin takarar na cikin muhimman abubuwan da za su tattauna.