Sojojin Najeriya a Jihar Borno sun cire haramcin da suka saka na hawa keke a Ƙaramar Hukumar Dikwa.

Rundunar sojin haɗin gwiwa mai lamba 24 da ke Dikwa a Jihar Borno wadda ke aiki a ƙarƙashin rundunar Operation Hadin kai ce ta saka dokar tun da farko.


Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa an saka dokar ne bayan kashe masu sana’ar gwan-gwan 23 a ƙauyen Mukdala inda ake zargin mayaƙan Boko Haram ne suka kashe su.


An kashe su ne ta hanyar yi musu kwanton ɓauna wanda hakan ne ya sa sojojin suka saka haramcin hawa keke domin daƙile wannan matsalar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *