Shugaban kasa Muhammadu zai jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron kasashe rainon Ingila wato Commonwealth na 2022 wanda aka shirya gudanarwa a Kigali, kasar Rwanda, a mako mai zuwa.

Stanislas Kamanzi, babban kwamishinan Rwanda a Najeriya ne ya bayyana hakan a wajen taron sada zumunta na kafin taron na CHOGM 22 da aka gudanar a Abuja.


Yace Kasar Rwanda da mutanenta sun shirya karbar bakuncin daya daga cikin manyan tarukan duniya tare da manyan shugabanni da tawagoginsu da za su hallara.


Kamanzi ya bayyana cewar taron zai zama wani dandalin muhawara da daukar matakai kan batutuwan na gama gari, wadanda suka hada da shugabanci da bin doka; kiyayewa tare da alaka tsakanin tattalin arziki da muhalli; lafiya; fasaha da matasa.


Babban kwamishinar Birtaniya a Najeriya, Catriona Laing, ta ce a yanzu Birtaniya a shirye take ta mikawa kasar Rwanda shugabar kungiyar Commonwealth bayan shekaru hudu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *