Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fitar da wani daftarin dokoki ga kamfanonin shafukan sa da zumunta na Tuwita da Facebook da WhatsApp da Instagram da Google da TikTok da sauransu kan ayyukansu a ƙasar

Dokokin, waɗanda aka samar da su don sa ido a kan yadda shafukan sa da zumuntar ke aiki, sun bayyana cewa dole kowane kamfani da ke aiki a Najeriya ya samar da duk bayanansa.


Sannan dole ya taimaka wa duk wata hukuma ta gwamnati da abin da take buƙata da nufin aiwatar da bincike ko shawo matsalolin laifukan intanet ko kuma shigar da ƙara a kan laifi.


Gwamnatin tana kuma so shafukan sa da zumuntar su kiyaye dokokin Najeriya kuma kar su yi duk wani abu ko wata kwaskwarima da za su yi katsalandan ga dokokin ƙasar.


Hukumar Ci gaban Fasahar Sadarwa ta Najeriya NITDA ce ta fitar da sababbin sharuɗɗan, sakamakon umarnin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *