Gamayyar Kungiyoyin fararen hula na Arewacin Najeriya sun gargadi Yan Arewa da kada a rudesu da nagartar jam’iya a Zaben 2023 maimakon hakan su zabi mutum .

Haka Kuma kungiyoyin sunyi gargadi da kada su biyewa zantukan wasu mutane na cewa asarar Kuria ne a zabi Wanda ake ganin bazai kai labari ba a zabukan na badi komai nagartarsa.


Shugaban gamayyar Kungiyoyin fararen hula na Arewacin Najeriya Com Nastura Ashir Sharif shine yayi wanna gargadin a wani taron manema labarai da kungiyar ta Kira a birnin Kano.Haka Kuma Nastura Sharif yace idan ta kama kafin Zaben na 2023 zasu iya kama sunanyen mutanan da ya kamata Yan Arewa su zaba .


Ya kuma yi gargadi game da karancin fita ayi rijistar samun katin zabe daga Arewacin Najeriya.


Ya hakurkurtar da Yan Arewa dasuyi amfani da damar da ta rage wajen yin rijistar samun katin zaben yana Mai cewa su manta abinda ya faru a baya na rashin kyautata musu suyi fata Mai kyau anan gaba sannan kada su yanke tsammani daga samun rayuwa Mai kyau anan gaba .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *