Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP mai kayan Dadi Engr Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi alkawarin magance matsalar rashin tsaro da samar da ingantaccen ilimi a kasar nan idan yayi nasarar lashe zaben 2023.

Dr Rabiu Kwankwaso wanda tsohon ministan tsaro ne ya kuma ce zai bullo da kyawawan manufofin tattalin arziki da za su ciyar da kasa gaba.


Sannan a bangaren Ilimi yaci alwashin cewa kamar yadda ya dauki nauyin kai matasa karatu kasashen waje ,da zarar ya zamo shugaban kasa zai dora,tare da mayar da ilimin cikin gida daga Furamare har Jami,a kyauta.


Sannan ya koka abisa yadda har yanzu daliban kasar nan suke zaman gida sama da wata biyar saboda yajin aikin malaman Jami,oi ASUU.


Sanata Kwankwaso yana daukar wadannan alkawura ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a cibiyar Kolanut, a wata ganawa da wakilan jam’iyyar NNPP mai kayan marmari a babbar birnin Calabar a jihar Cross River.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *