Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke gargdain cewar ficewar sojojin Farnasar daga Menaka na iya jefa yankin cikin hadarin sake fadawa hannun ‘yan ta’adda.
Kakakin rundunar sojin Faransa Janar Pascal Ianni ya ce an kammala janyewar sojojin nasu daga sansanin cikin kwanciyar hankali, ba tare da samun wata matsala ba.
Janar Ianni ya ce ficewar dakarun na zuwa ne kafin kammala janyewar sojojin Faransa daga kasar kamar Mali baki daya kamar yadda aka tsara a bazarar bana, wanda zai kunshi mika sansanin sojin dake Gao hannun sojojin kasar da kuma kawo karshen aikin rundunar Barkhane.