Waɗannan matsaloli za su zo ne a yayin da farashin ɗanyen fetur ya kai dala 120 duk ganga ɗaya, lamarin da ake sa ran zai amfani waɗannan ƙasashen da dama su ne manyan ƙasashen Afirka da suka fi samar da fetur.
A wani rahoto da Babban Bankin Duniya ya fitar a ƙarshen mako, ya ce “A ƙasashen kudu da hamadar Sahara da dama, za a samu hauhawar farashi da da ƙarancin wutar lantarki da ƙarancin abinci da man fetur.
Wannan batu na zuwa ne a daidai lokacin da dama Najeriya ke fuskantar matsannacin hauhawar farashi da ƙarin samun layuka a gidajen mai a faɗin ƙasar nan.