Shugaban Ƙungiyar ASUU Farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyana haka a cikin wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa a Najeriya a ranar Litinin a Abuja.
ASUU ta kasance tana Yajin aiki na tsawon watanni 5 domin neman a biya mata buƙatun ta.
Malaman Jami’o’in sun shiga Yajin Aiki da suka haɗa da kuɗaɗen tafiyar da harkokin Gwamnati, da Kuɗin Alawus-Alawus, da manhajar biyan Albashi ta UTAS.
Sauran sun haɗa da yarjejeniyar ASUU na Shekarar 2009, da rashin dai-dai akan hanyar biyan kuɗi ta IPPIS.