Kungiyoyin dai sun ce hukumar zaben kasar na da ƙarancin wadatattun ma’aikatan da suka kamata wajen yi wa ‘yan kasar rijista, da ƙalubalen da ke tattare da na’urorin da ake amfani da su wajen yin rijistar.
Jihar Kano na daga cikin jihohi a Najeriya da ake da ƙarancin waɗanda ba su fito yin katin zaɓen ba, inda kungiyoyin su ma suka alaƙanta hakan da gajen haƙurin waɗanda suka yi rijista zuwa ofishin hukumar zabe don a dauki bayanansu.