Sanata Shehu Sani ya tada kura a intanet, yayin da ya nemi Obasanjo ya zabi Atiki ko Tinubu.

Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar wakilai ta takwas, Shehu Sani, ya ce ya tambayi tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya zabi dan takarar shugaban kasa kafin zuwan 2023.

Sani a wani sako da Rahma ta gani a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, 13 ga watan Yuni, ya ce ya roki Obasanjo ta Whatsapp da ya zabi dan takara tsakanin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da Bola Ahmed Tinubu.

Tsohon sanatan ya kara da cewa zai yi wa mabiyansa bayani a dandalin sada zumunta idan tsohon shugaban kasar ya amsa masa. Atiku da Tinubu su ne ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP da APC a zaben 2023 mai zuwa, jam’iyyu biyu mafi tasiri a Najeriya.

Sanata Sani ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa:

“Na aika da sakon WhatsApp ga Baba Obasanjo ya zaba daga cikin jiga-jigan nan biyu. Idan ya amsa, zan sanar da ku. Idan ba ku ji ta bakina ba, hakan na nufin har yanzu bai ba da amsa ba.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.