Rundunar tsaro ta DSS ta tabbatar da kama kama wani da take zargin ɗaya ne daga cikin manyan kwamandojin kungiyar ISWAP a Kano.

Rundunar tsaron ta dai kama wanda ake zargin tare da wasu daga cikin yaransa a daidai lokacin da suke shirya kai wasu hare-hare na ta’addanci a Kano.

Mutumin, wanda jami’an DSS suka kama da ake yi wa laƙabi da Malam Abba, an kama shi ne a unguwar Samegu a yankin karamar hukumar Kumbotso a Kano.

DSS ta ce ta sami nasarar kama Malam Abba da waɗanda aka kama shi da su bayan samun wasu bayanan sirri.

Sannan wanda ake zargin shi ne mai bayar da horo, da shirya hare-haren da ISWAP din za ta kai a jihar.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da babban hafsan tsaro Najeriya janar Lucky Irabor ke cewa rudunar tsaron kasar ta daƙile wani yunƙurin kai hari a Kano wanda suka ce zai iya zama “mafi muni” a ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *