Masu fafutukar wajen nuna adawa da manufofin gwamnatin Birtaniya na tura bakin haure zuwa Rwanda sun ce za su daukaka karar su zuwa kotun daukaka kara a litinin din nan.

Hakan na zuwa ne bayan da babbar kotun kasar ta ce jirgin farko dauke da masu neman mafaka kimanin 31 daga Birtaniya zai nufi kasar Rwanda ranar Talata, kafin wasu su bi sahu daga bisani.

Sai dai masu fafutukar da suka shigar da karar ta farko a babbar kotun, sun ce sun damu matuka kan halin da mutanen da aka shirya tilasta maida su gida zasu shiga don haka su ke kokarin hana tashin jirgin na farko.

Da yake magana a babban kotun a ranar Juma’a, Justice Swift ya ce bayyi la’akari da akwai wata hujja da zai sanya a ki kulada masu neman mafaka ba.

Sai dai ya ce za a sake nazarin shari’ar, inda babbar kotun za ta saurari daukaka karar manufar baki daya, kafin karshen watan Yuli.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *