Haraji mai tsanani da ƙungiyar al-Qaeda mai ƙawance da al-Shabab ta ƙaƙaba wa mutane a wasu yankunan Somaliya ya sa manoma ba sa iya girbe amfanin gonarsu a yayin da ake fama da matsannacin fari.

Abdirahman Abdishakur Warsame, jakada na musamman ga shugaban ƙasar
Hassan Sheikh Mohamud a kan batun farin, ya ce harajin na al-Shabab na tursasa
wa manoma tserewa su bar gonakinsu da gidajensu.

Mr Warsame ya shaida wa shugaban ƙasar da shugabannin gundomomin ƙasar
hakan ne a jiya Lahadi a wani taro da aka shafe kwana biyu ana yi.

Ya ce fiye da ƴan Somaliya miliyan bakwai ne fari ya shafa. Kuma mutum 250,000
daga cikinsu na fuskantar matsananciyar yunwa.

Al-Shabab na yawan amfani da yunwa da ake fama da ita a ƙasar don ƙara fito da
kanta da kuma bayar da tallafi ga jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *