Kungiyar ta CAN tayi wannan Kiran ne sakamakon harin da aka Kai wata majamia dake Owo a jihar Ondo a Ranar Lahadin data gabata inda mabiya addinin Kirista 40 suka mutu wasu da dama suka jikkata.
A wata takardar bayan taro da kungiyar ta CAN ta rabawa manema labarai tace baiwa daidaikun jama’a damar mallakar Bindiga a ko ina a cikin Kasar Nan zai taimawa jamaa su rika Kare kansu daga hare hare.
Kungiyar ta Kara da cewa ya kamata gwamnatin Tarayya tayiwa dokar haramtawa Yan Najeriya mallakar Bindiga kwaskwarima ta yadda kowa zai mallaki bindigar Dan ya Kare kansa.
Wasu Yan Najeriya da dama suna ta kalubalantar kungiyar ta CAN a sassan Kasar Nan , ganin yadda take ta babatu akan harin da aka Kai cikin majamiar a makon da ya gabata a jihar ta Ondo , inda wasu suke ganin beken kungiyar kiristoci ta kasa CAN saboda yadda shugabaninta sukaja bakinsu sukayi shuru a iya shekarun da aka dauka ana kashe kashe a Arewacin Najeriya ciki harda wuraren Ibada .
Kungiyar ta CAN tayi wannan Kiran ne sakamakon harin da aka Kai wata majamia dake Owo a jihar Ondo a Ranar Lahadin data gabata inda mabiya addinin Kirista 40 suka mutu wasu da dama suka jikkata.
A wata takardar bayan taro da kungiyar ta CAN ta rabawa manema labarai tace baiwa daidaikun jama’a damar mallakar Bindiga a ko ina a cikin Kasar Nan zai taimawa jamaa su rika Kare kansu daga hare hare.
Kungiyar ta Kara da cewa ya kamata gwamnatin Tarayya tayiwa dokar haramtawa Yan Najeriya mallakar Bindiga kwaskwarima ta yadda kowa zai mallaki bindigar Dan ya Kare kansa.
Wasu ‘yan Najeriya da dama suna ta kalubalantar kungiyar ta CAN a sassan Kasar Nan , ganin yadda take ta babatu akan harin da aka Kai cikin majamiar a makon da ya gabata a jihar ta Ondo , inda wasu suke ganin beken kungiyar kiristoci ta kasa CAN saboda yadda shugabaninta sukaja bakinsu sukayi shuru a iya shekarun da aka dauka ana kashe kashe a Arewacin Najeriya ciki harda wuraren Ibada .