Dubban jama’a a ne suka yi zanga-zanga a Washington DC da sauran sassan Amurka inda suke rajin ganin an bullo da dokoki masu tsauri na mallakar bindiga.

Matakin ya biyo bayan jerin kisan tarin mutane da aka yi ne ta hanyar amfani da bindiga a kasar a cikin kwanakin nan, abin da masu fafutuka ke cewa za tilasta wa majalisar dokokin Amurkar daukar mataki.

Taken wannan gangami dai shi ne, ”Wannan lokacin zai zama daban.” Tsawon shekaru dai majalisar dokokin Amurkar ta ki daukar matakin yin dokokin takaita mallakar bindiga a kasar wanda zai kai ga rage aikata ta’asar da ‘yan bindiga-dadi kan tafka.

Masu rajin mallakar bindiga da kuma ‘yan jam’iyyar Republican ne kan yi wa ‘yan majalisar tarnaki a kan hakan.

To amma harbin da dan bindiga-dadi ya yi a wata makarantar furamare a Texas inda ya hallaka yara 19 hadi da malamansu biyu, ya sauya salon muhawarar da ake yi a kan batun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *