A kullum ina rayuwa cikin bakin ciki da damuwa saboda matsalar tsaro – President Muhammadu Buhari.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Lahadi, 12 ga watan Yuni, ya nuna damuwa kan matsalar rashin tsaro a kasar Najeriya.

Buhari ya bayyana cewa a kullum yana rayuwa cikin damuwa da bakin ciki saboda wannan kalubale na tsaro da ya yiwa kasar katutu.

Ya yi kira ga al’ummar Najeriya da su dage da addu’o’i tare da ba hukumomin tsaro hadin kai domin kawo karshen wannan lamari.

Ya ce:

“Don cimma wannan, dole sai dukkanmu mun bayar da gudunmawa. Ba aiki gwamnati bane ita kadai. Ina bukatar dukkanin al’ummar kasar da su taimaka sannan su ba hukumomin tsaronmu hadin kai ta hanyar kai rahoton duk wani abun da basu yarda da shi ba ga hukumomin tsaro. Za mu samu kasa mai tsaro ne kawai idan muka yi nasarar hana laifuka bawai bayan an aikata laifi ba.

“A wannan rana ta musamman, ina so dukkanmu mu sanya wadanda ayyukan ta’addanci ya ritsa da su a zukatanmu da addu’o’inmu. A kullum ina rayuwa cikin bakin ciki da damuwa saboda wadannan mutane da wadanda ke garkame sakamakon ta’addanci da garkuwa da mutane. Ni da hukumomin tsaro muna yin duk mai yiwuwa don kubutar da wadannan maza da matan cikin koshin lafiya”.

Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta gyara wasu tsare-tsaren tsaro na kasar.

Ya ce:
“Wasu daga cikin kadarorin tsaro da muka sayo shekaru uku da suka gabata sun iso kuma an tura su wurare. Ana habbaka tsarin tsaro na yanar gizo da tsarin sa ido don kara habbaka ikon mu na bin diddigin masu aikata laifuka. Muna kuma daukar sabbin ma’aikata da horar da su a dukkan hukumomin tsaro da na leken asiri domin karfafa tsaron kasar baki daya.”

President Muhammadu Buhari, June 2022.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *