Yan ta’ada da suka kai hari jirgin kasa Kaduna zuwa Abuja sun sako wasu daga cikin fasinjojin da suka.sace bayan kwanaki 74 da yin garkuwa da su

Yan ta’addan da suka kai har jirgin kasan Abuja-Kaduna sun sako wasu daga cikin mutum sama da sittin da suka kwamushe ranar 28 ga Maris, 2022.

Mai gidan jaridar Desert Herald, Tukur Mamu, wanda ya bayyana hakan yace mutum goma sha daya (11) aka sako ranar Asabar, 11 ga Yuni, 2022., rahoton Daily Trust.

Amma yace majiyoyinsa suna mazajen da aka saki na fama da rashin lafiya ne yayinda matan da aka sake marasa karfi ne kamar yadda akayi yarjejeniya da yan bindigan.

Yace:

“Abinda aka sa rai dama shine su saki dukkan matan da suka sace a karon farko amma sai suka rage adadin matan da zasu saki saboda gwamnatin Najeriya ta bukaci a saki masu jinya.”

A ranar 28 ga watan Maris ne ‘yan ta’addan suka halaka fasinjoji tara gami da garkuwa da mutane da dama bayan lalata jirgin kasa a wani kilomita kadan daga Kaduna, babban birnin jihar Kaduna. Daga bisani sun sako wasu daga ciki, tare da barin 62 a hannunsu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *