Rundunar ’yan sanda a Jihar Kano ta cafke wasu mutum biyar da ake zargi da yi wa wani dan kasar Indiya fashi da makami a jihar

Ana zargin mutanen da shiga gidan mutumin da ke unguwar Sharada a Karamar Hukumar Birni.

Da ya ke gabatar da masu laifin ga maneman labarai a Kano, kakakin ‘yan sandan Jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an cafke su ne yayin wani sintiri.

Tawagar ‘Puff Adder’ karkashin jagorancin SP Abdulrahim Adamu, ne suka gudanar da sintiri a yankin Sharada,dake Karamar Hukumar Birnin, inda suka tare wani babur mai kafa uku dauke da wani mutum guda daya a kofar gidan wani dan kasar Indiya.


Kiyawa ya kara da cewar an kama wasu a cikin gidan dan kasar Indiyar yayinda suke masa fashi.


A cewarsa za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu don gudanar da bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *