Shugabannin ASUU sunki amincewa jama’a suyi karo-karon kudade domin biyawa kungiyar bukatun da suka sa ta shiga yajin aiki ne bayan an yi musu tayin hakan a safiyar ranar Asabar.
Hakan ya biyo bayan karbar bakuncin kungiyar a shahararren shirin Brekete Family wanda gidan rediyon Human Rights ke gabatarwa a Abuja.
Shirin ya gayyato Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke da jami’an kungiyar ne domin su yi wa ’yan Najeriya bayanin dalilin yajin aikin da ya ki ci, ya ki cinyewa.
Shahararren mai gabatar da shirin, Ahmed Isah, ya kafa asusun tara wa kungiyar kudade domin share mata hawaye ta janye yajin aiki.
A lokacin tattaunawar ta ranar Asabar, Ahmed Isah, ya gabatar da Naira miliyan 50 da Gwamnan Jihar Akwa-Ibom, Udom Emmanuel, ya bayar domin sanyawa a asusun tallafin da aka bude.
Nuna kudaden a baiwar jama’a ke da wuya, shugaban kungiyar ya nesanta kungiyar da kudaden da ake tarawa.