Toshon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan, ya taya Bola Tinubu murnar zama dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar APC mai mulki.

Jonathan wanda a yi ta cece-ku-ce kan yiwuwar fitowarsa neman takarar shugaban kasa a APC ya kuma taya tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, murnar samun tikitin takarar shugaban kasa a Jam’iyyar PDP.

Ya taya ’yan takarar shugaban kasar manyan jam’iyyun siyasar Najeriya murna ne a sakon da ya fitar a ranar Juma’a ta shafinsa na Twitter.

A cewarsa, “Yayinda kuke ci gaba da yakin neman zabe, yana da kyau al’amuran da suka addabi kasarnan da ingantattun hanyoyin magance su su dauki matakin farko.

A Sakon tara murna ya taya wadanda suka samu nasara a zabukan fidda gwani a fagen siyasa, musamman Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Peter Obi na Jam’iyyaram’iyyar Labor, da Asiwaju Bola Tinubu na Jam’iyyar APC.

Haka kuma, da jiga-jigan wasu jam’iyyun da su ma suka kammala zaben fidda gwanin da suka hada da Sanata Rabi’u Kwankwaso na Jam’iyyar NNPP da Malik Ado-Ibrahim na YPP da Cif Dan Nwanyanwu na ZLP da Dumebi Kachikwu na ADC da kuma Adewole Adebayo na jam’iyyar SDP.

Leave a Reply

Your email address will not be published.