Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC da sauran ‘ya’yan jam’iyyar dasu hada kai domin tabbatar da nasarar Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa a
jam’iyyar.
Shugaba Buhari, a wata wasika da ya aikewa shugaban kungiyar gwamnonin kasarnan, Atiku Bagudu, yace Tinubu ba bako bane a idon gwamnonin.
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa, Garba Shehu, ne ya fitar da sashen wasikar a jiya Alhamis.

A cikin wasikar, shugaba Buhari ya yabawa gwamnan jihar Kebbi, wanda ya kasance shugaban kwamitin zaben fidda gwanin da aka kammala, bisa kwarewa da kuma yadda ya gudanar da zaben fidda gwanin cikin lumana.
Shugaban ya ce yana fatan yin aiki da gwamnonin domin ganin Tinubu ya lashe zaben 2023.