Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin 13 ga watan Yuni a matsayin ranar hutu domin bikin ranar Dimokuraɗiyya ta wannan Shekarar.

Ministan Cikin Gida Rauf Aregbesola ne ya bayyana haka a madadin Gwamnatin Tarayya, cikin wata sanarwa daya fitar a kafafen yaɗa labaru a ranar Alhamis.

Ya taya ƴan Najeriya murnar zagayowar wannan rana, tare da yin kira a garesu dasu goyi bayan wannan Gwamnati a ƙoƙarin ta na samar da tsaro, haɗin kai da zaman lafiya.

Ministan yayi kira ga ƴan Najeriya dasu yi amfani da Manhajar da aka fitar wanda za’a yi amfani da’ita domin magance matsalolin tsaro da sauran bala’o’i a Ƙasarnan.

Ya kuma bada tabbacin cewar Gwamnatin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari na iya kokarinta wajen tsare rayuka da dukiyoyin Al’umma, da kuma bunkasa Tattalin Arziki, Ƙasarnan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *