Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutune 32 sakamakon harin bindiga a wasu yankunan hudu da ke jihar.

Yankunan sun hada da Unguwan Gamu da Dogon Noma da Ungwan Sarki da Maikori, duk a karamar hukumar Kajuru.

Sai dai gwamnati ta musanta rahotanni da ke cewar an kai harin ne da manyan makamai da jirgin helikwafta.

Mazauna yankin na cewar helikeafta ya taimakawa maharan wajen kutsawa kauyuka a ranar Lahadi.

Kwamishinan harkokin cikin gida da Tsaro, Samuel Aruwan ya ce babu gaskiya a rahoton da ke cewar ‘yan bindiga sun kai hari da helikwafta.

Leave a Reply

Your email address will not be published.