Gwamnan Jihar Anambra Farfesa Charles Soludo yace kimanin Malaman Makaranta 1,000 aka dakatar daga aiki, sakamakon rashin cancantar su wajen gudanar da aikin su.

Gwamnan yace waɗanda aka dakatar basu cancanta su riƙa koyarwa ba.

Soludo ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Sakataren a kafafen yada labarai Chris Aburime ya Fitar.

A cewarsa babu wani Malamin Makaranta daya cancanta da aikin, yayin da gwamnatin Jihar ta dauki matakin dakatar dasu.

Gwamnatin jihar Anambra ta sanar da guraben ɗaukar Malamai da Ma’aikatan Lafiya guda dubu 5,000, inda sama da mutane dubu 31,500bzasu zana Jarabawar, a ranar Asabar mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *