Bayan tattaunawa da Osinbajo, ya kuma ziyarci shugaba Muhammadu Buhari.
Tinubu ya samu kuri’u 1,271 a zaben fitar da gwanin jami’yya APC da aka gudanar , inda ya doke sauran ‘yan takara ciki harda Osinbajo wanda ya samu kuri’u 235.

Ziyarar Tinubu na zuwa ne bayan Osinbajo ya mika sakon taya murna Tinubu da nuna mubaya’ar aiki tare dashi domin nasara a babban zaben 2023.