Bayan janye wa Tinubu, tsohon ministan harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio, ya lashe tikitin takarar sanata na jam’iyyar APC.

Tsohon ministan harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio, ya lashe tikitin takarar Sanata mai wakiltar Akwa Ibom ta arewa maso yamma a jam’iyyar All Progressive Congress wato APC.

Daily Trust ta ruwaito cewa Akpabio, wanda ya janye wa Bola Tinubu a zaben fidda ɗan takarar shugaban kasa da aka kammala, ya samu nasara ne da kuri’u 478.

Da yake jawabi ranar Alhamis da daddare a Cibiyar tallafawa al’umma ta Godswill Akpabio da ke karamar hukumar Ikot Ekpene, wato wurin da aka canza zaben, tsohon ministan ya gode wa mutane bisa ganin cancantarsa.

Akpabio ya ce:

“Ina gode wa mutanen mazaɓar Akwa Ibom ta arewa maso yamma bisa ganin na cancanta ku sake bani damar wakiltar ku a majalisar dattawan Najeriya. Na tuna lokacin da kuka bani irin wannan damar tsakanin 2015 zuwa 2019.”

Bayan janye wa Tinubu, tsohon ministan harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio, ya lashe tikitin takarar sanata na jam’iyyar APC.

“Zan iya tuna cewa babu wani Sanata da ya tallafa muku kamar yadda na tallafa muku. Na san ayyukan da aka yi a sassan ƙananan hukumomi 10, tun daga na kasuwanni har da ayyukan ruwa, wuta, gini, da gina ɗakunan karatu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *