Ana sa ran Tinubu zai dauki Mataimaki ne daga Arewacin Najeriya yayin da ya gana da Gwamnonin jam’iyyar daga Arewacin Najeriya a jiya Alhamis.

Ganawar na zuwa ne a daidai lokacin da dan takarar ke ta kokarin daukar wanda zai dafa masa a takarar da zai’yi a zaben 2023 mai zuwa.

Kasancewarsa wanda ya fito daga Kudancin Najeriya, ana saran dai Tinubu zai dauki Mataimaki ne daga Arewacin Najeriya.

Gwamnonin Arewa na jam’iyyar APC sun taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar Tinubu a takarar, musamman yadda suka tsaya kai da fata sai kujerar takarar.

Tuni dai Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ta baiwa jam’iyyu wa’adin mako daya da su mika sunayen wadanda za suyi musu Mataimaka a takarar tasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *