Zaben fidda gwanin APC: “Babu wanda zai iya ba mutum mulki sai Allah. Zan amshi sakamakon da zuciya daya”. – Yerima

Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma mai neman takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC),

Ahmad Yerima, ya yi alkawarin karbar sakamakon zaben fidda gwani da zuciya daya. Yerima ya fada ma kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Eagle Square, filin babban taron jam’iyyar cewa yana fatan samun tikitin jam’iyyar a karshen taron .

Yace:

“Ina fatan cewa zan lashe zaben, amma duk abun da ya faru, shine nufin Allah”

“Babu wanda zai iya ba mutum mulki sai Allah. “Don haka, duk abun da ya faru, shine nufin Sa kuma zan karbe shi da hannu bibbiyu.” Vanguard ta kuma rahoto cewa Yerima ya jinjinawa shugabancin jam’iyyar da ya shirya babban taro na lumana.

“Da izinin Allah, ingantaccen dan takara zai bayyana ga APC, koda ba ni bane.

“Da zaran an kammala zaben, wani zai bayyana. Ana sanya ran dukkanin yan takarar da basu kai labari ba za su karbi lamarin da kyau.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.