Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya gargadi jam’iyyar APC, cewa cire sunansa a jerin ‘yan takarar shugaban kasa da za su gwabza a zaben fidda gwani na yau daidai yake yake da kunno wutar rikici, Vanguard ta ruwaito.
Gwamna Bello, wanda yana daya daga cikin ’yan takara 23 a jam’iyyar, ya ce akwai makarkashiyar da ake shirya masa, inda ya zargi gwamnonin APC na Arewa da wasu jiga-jiga da kitsa manakisa akansa.
Shugaba Buhari ne kadai zai sa na janye – Yahaya Bello
Bello wanda ya bayyana kansa a matsayin dan takara mafi karbuwa da zai yi nasara idan har tsarin ya tafi daidai, ya ce abu daya ne zai hana shi ya tsaya takarar shugaban kasa shi ne idan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya janye daga takarar, inji The Nation.
Da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnati bayan ganawar sirri da shugaban kasa, Bello ya ce jam’iyyar APC za ta ci gaba da rike madafun iko idan har ta yi bi ka’ida. A kalamansa:
“Shigowa cikin fage a yau, zan yi nasara sosai idan tsarin ya tafi daidai.”
Ya ce babu bukatar a cire shi a zaben fidda gwanin, yana mai bayyana cewa, yana wakiltar matasa da wadanda aka zalunta ne.
Bello ya ce gwamnonin APC na Arewa ba su tuntube shi ba a lokacin da suka dauki kudurin cewa mulki ya koma Kudu, kuma kudurin bai masa ba.
Ya kuma kara jaddada adawarsa ga tsarin shugabancin karba-karba, yana mai cewa hakan ba zai bayar da damar samun wanda ya cancanta ya tafiyar da al’amuran kasar nan ba.