Mai Magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina, yace ya yanko maganar da shugaba Buhari ya fada a wata takarda da aka fitar a ranar Litinin.
Adesina yace Zaben fidda ‘dan takarar shugaban kasar wanda za a gabatar a ranar 7 ga watan Yuni ya riga ya kankama.
Yayin da Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar APC na kasa ya ayyana shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan a matsayin ‘dan takarar shugaban kasar jam’iyyar,
gwamnonin jam’iyyar sun hakikance akan cewar dole a ba kudu tikitin tsayawa takarar shugaban kasar.
Ya kara da cewar, wakilan zaben za suyi kokarin ganin sun zabi wanda ya dace gami da daukar wanda zai rike tutar jam’iyyar don ganin an yi nasara a 2023.