El-Rufai ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da manema labarai a jiya Litinin bayan gwamnonin sun kammala ganawarsu da shugaban kasa Buhari.
Da yake jawabi ga manema labarai, El-Rufai ya ce gwamnoni 13 daga cikin 19 na jami’yyar APC daga Arewa sun amince da cewar a mika tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar zuwa yankin Kudu.
Gwamnan na Kaduna, ya ce gwamnan na kogi wanda dan takarar shugaban kasa ne na jami’yyar APC, ya yanke shawarar kin halartar taron.
A cewar El-Rufai, gwamnan jihar Kogi ya ki amincewa da matakin da takwarorinsa suka dauka na mika tikitin takarar shugaban kasa a yankin Kudu.
Sai dai, anasa jawabin, shugaban kungiyar gwamnonin Atiku Bagudu, ya ce zai kawo zaman lafiya akai tikitin takarar shugaban kasa yankin Kudu.