Dan takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce zaben 2023 zai zama raba gardama dangane da ayyukan da gwamnatin APC ta yiwa kasa a tsawon lokacin da tayi tana rike da mulki

Atiku yace abin damuwa ne yayinda jama’a ke cikin jimami da bakin cikin mummunan harin da aka kai a garin Owo na Jihar Ondo, yayinda jami’yyar APC ta kasa soke liyafar data shiryawa ’yan takararta na Shuagaban Kasa.


Cikin sanarwar daya fitar ta hannun kakakinsa, Paul Ibe, Atiku yace duk yadda aka zubar da jinin masu ibadar daba suji ba basu gani ba a Jihar Ondo, wannan bai hana shugabannin jami’yyar APC haduwa ba’a Abuja don yin shagalinsu wanda hakan yayi nuni da rashin tausayin halin da kasa ke ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *