Dan shekara biyu ya harbui mahaifinsa har lahira yayin da yake wasa da bindiga a Amurka.

Wani yaro dan shekara biyu ya harbe mahaifinsa har lahira a Amurka yayin wasa da bindigar da iyayensa suka ajiye, hukumomi a birnin Florida ta Amurka suka bayyana ranar Litnin.

Yayin da jami’an yan sanda suka dira gidan ranar 26 ga Mayu, sun ga mahaifiyar yaron, Marie Ayala, na kokarin farfado da mijinta, Reggie Mabry, rahoton AFP.

Da farko jami’an tsaro sun dauka mahaifin ne ya harbe kansa amma daya daga cikin yaran gidan ya bayyanawa mahukunta cewa kaninsu dan shekara biyu ne yayi harbin, Shugaban hukumar yan sandan yankin John Mina ya bayyana haka a hira da manema labarai.

Yace:

“Masu bindiga basu ajiye makamansu da kyau kuma dan sakacin lokaci kadan sai kaji wani mumunan abu ya faru.” “Yanzu wadannan yaran sun rasa iyayensu duka. Mahaifin ya mutu. Mahaifiyarsu na kurkuku.”

Ire-iren wadannan abubuwa na faruwa a Amurka. A Agustan 2021, wani dan shekara biyu haka ya bindige mahaifiyarsa yayinda take waya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *