APC 2023: Ba zan janye wa kowa ba – Tunde Bakare.

Fasto Tunde Bakare ya ce bai shiga neman takarar shugaban ƙasa a APC ba don ya janye wa wani.

“Da yawa daga cikin waɗannan ‘yan takarar suna da matsala da hukumar EFCC,” in ji shi yayin da yake magana kan ƙwarewarsa a harkokin mulki.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake tabbatar da cewa bai taɓa riƙe wani muƙamin siyasa ba, amma ya ce “da yawa daga cikin waɗanda suke da ƙwarewar su suka lalata ƙasa [Najeriya]”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *