‘Yan bindiga ne sun sace mahaifiyar dan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a Jam’iyyar APC, Abdulkarim Abdulsalam Zaura a Karamar Hukumar Ungogo a Jihar Kano.

’Yan bindiga ne sun sace mahaifiyar dan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a Jam’iyyar APC, Abdulkarim Abdulsalam Zaura a Karamar Hukumar Ungogo a Jihar Kano.


’Yan bindigar sun kai farmaki gidan dan takarar Sanatan na APC ne da sanyin safiyar yau Litinin, suka yi awon gaba da mahaifiyarsa, Hajiya Laure.


Shugaban Karamar Hukumar Ungogo, Injiniya Abdullah Garba Ramat, ya tabbatar da faruwar lamarin a shafinsa na Facebook.


Mai magana da yawun bakin ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Kiyawa ya shaida cewa sun tura dakarun Puff Adder zuwa wannan yanki.


SP Abdullahi Kiyawa ya na sa ran rundunar ‘yan sandan jihar su iya ceto wannan Baiwar Allah, sannan su damke wadanda suka dauke ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published.