Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa hatsarin mota bai ritsa da shi ba kamar yadda ake ta rade-radi.

Osinbajo ya bayyana cewa sun ci karo da wani hatsari da aka yi ne a hanyarsu ta zuwa filin jirgin sama don haka sai suka tsaya domin taimakawa wadanda lamarin ya ritsa da su.


Ya bayyana cewa jami’an tsaronsa da tawagar likitocinsa sun taimaka wajen kwashe mutanen da suka yi hatsarin daga wajen da lamarin ya afku, sannan suka mika su asibitin sojoji.


A wannan rana ta Litinin ne aka fara yada labarin cewa Farfesa Osinbajo ya yi hatsari a kan hanyarsa ta zuwa jihar Ondo don jajanta wa iyalan waɗanda aka kai wa hari a Cocin Francis a Owo a jiya Lahadi.


A wani saƙon tuwita da ya wallafa, Akande ya ce mataimakin shugaban ƙasar ya ga wani hatsari ne da aka yi a hanyarsa ta zuwa filin jirgin saman Abuja, inda ya tsaya don ya taimaka wa waɗanda abin ya rutsa da su.


Ya ƙara da cewa tuni Osinbajo ya isa jihar Ondon inda yayi abin da ya kai shi.


Ita ma hukumar kula da kare afkuwar haɗurra ta Najeriya ta ƙaryata batun cewa Osinbajo ne ya yi hatsarin, kamar yadda aka yi ta yaɗawa a kafafen sada zumunta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *