Gwamana Yahaya Bello na jihar Kogi, ya ce yan takarar shugaban ƙasa ana APC sun amince su goyi bayan duk wanda Shugaba Buhari ya zaba ya gaje shi.

A ranar sabar data gabata, Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya gana da baki ɗayan yan takara a fadarsa da ke babban birnin tarayya Abuja.


A taron Buhari ya bukace su da su yi maslaha a tsakanin su, su fitar da ɗan takara guda kafin ranar zaɓen fidda gwani, kamar yadɗa jaridar The Cable ta ruwaito.


Gwamana Yahaya Bello, ɗaya daga cikin masu hangen kujerar ta shugaban ƙasa, ya ce a shirye yake ya koma bayan wanda Buhari ya zaɓa daga cikin su.


Ayayin da aka tambaye shi ko Bola Ahmed Tinubu, ya na cikin waɗan da suka amince da haka, Bello ya ce ya halarci taron kuma bai musa ba.


,saboda haka idan wani ya yi magana a madadinka kuma baka da wani abu da ya saɓa wa haka, sannan ka yi shiru, hakan na nufin ka yarda.


Bugu da ƙari, Bello ya ce matsayar da gwamnonin arewa suka cimma na kai tikitin takara kudu bai shafe su ba kwata-kwata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *