Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya shawarci masu neman takarar shugabancin ƙasar a jam’iyyar APC dasu sasanta a tsakaninsu don amincewa da mutum guda ya wakilci jam’iyyar a zaɓen shugaban ƙasar da ke tafe.

Shugaban ya ba su shawarar ne yayin wata ganawa da ya yi da su da daren jiya Asabar a fadarsa da ke Abuja.


Dukkannin masu neman takarar sun halarci wannan ganawa, ciki har da jagoran jam’iyyar Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, wanda a baya-bayan nan ya furta wasu kalamai kan shugaban, da suka tayar da ƙura.


To amma kakakin shugaban Malam Garba Shehu bai kore yiwuwar hakan ba, inda yace idan shugaban ya yi shawara da waɗanda suka kamata to akwai yiwuwar a yi irin abinda aka yi lokacin zaben shugaban APC da aka yi baya bayan nan, inda Buharin ya goyi bayan Abdullahi Adamu a ƙurarren lokaci.


Kafin ganawar da shugaba Buhari ya yi da ƴan takarar dai wata sanarwar hadin guiwa da wasu gwamnonin APC 11 na arewa suka fitar, ta bukaci dukkannin masu neman takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar su janye don miƙawa yankin kudu mulki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *