Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin taron da ya yi da masu neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar mai mulki.
Rahotanni na cewar shugaban kasar ya ce bangaren Action Congress of Nigeria, wato ACN, na jam’iyyar ya fitar da dan takarar shugaban kasa.
A yayin taron, shugaba Buhari ya bukaci gwamnonin jam’iyyar APC da masu neman takarar shugaban kasar dasu kasance cikin shiri domin zaben fidda gwani.
A yayin wani taro da shugaban kasar ya yi da gwamnonin a ranar Talata,shugaba Buhari ya bukaci a ramawa yankin kudu karamci wurin zaben magajinsa.
Baya ga mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu, sauran yan takarar sun hada da Sanata Lawan Ahmad da tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi, da Ogbonnaya Onu, da Godswill Akpabio da Chukwuemeka Nwajiuba suka halacci taran .
Saura sun hada da Sanata Ken Nnamani, da Dimeji Bankole,da Ibikunle Amosun, Ajayi Boroffice da Rochas Okorocha. Da Fasto Tunde Bakare, da Uju Ken-Ohanenye, da Nicholas Felix,da Ahmad Rufai Sani,da Tein Jack-Rich da kuma Ikeobasi Mokelu suma suna cikin yan takarar shugaban kasar.